Shin Har Yanzu Sanata Mohammed Hassan Dambu Yana Da Tasiri A Siyasar Zone B?
Sanata Mohammed Hassan Dambu na daga cikin fitattun ‘yan siyasar Jihar Yobe, musamman a Yobe South (Zone B), inda ya taɓa wakiltar mazabar a Majalisar Dattawa daga 2015 zuwa 2019.
A zaɓen 2019, Dambu ya kasance ɗaya daga cikin ‘yan siyasar da suka fi jan hankali a jihar, sai dai bai samu nasarar komawa Majalisar Dattawa ba bayan da Sanata Ibrahim Mohammed Bomai na APC ya kayar da shi.
Daga baya ya sauya sheƙa daga PDP zuwa APC a shekarar 2022, inda ya taka muhimmiyar rawa a siyasar jam’iyyar kafin zaɓen 2023.
Yayin da ake tunkarar zaɓen 2027, Dambu ya sake sauya jam’iyya, inda ya fice daga APC zuwa NDC, matakin da ya sake jawo hankalin masu bibiyar siyasar Yobe.
A yanzu, tambayar da mutane da dama ke yi ita ce: Shin har yanzu Dambu yana da irin farin jinin da tasirin siyasar da ya yi fice da shi a baya, musamman a Zone B?
Amsar wannan tambaya za ta fito ne a fili yayin da yaƙin neman zaɓen 2027 ke ƙara ƙaratowa, inda za a ga irin ƙarfin goyon bayan da yake da shi a tsakanin al'umma da masu zaɓe.
Comments
Post a Comment