Tun bayan fara gasar Yobe Spelling Bee 3.0, mutane da dama suna tambaya: "Da miye al'umma za su amfana da wannan gasa?"
A cewar Shugaban Kwamitin Shirya Gasar (LOC), Abubakar K. Zaid, amfanin gasar ya fara bayyana tun kafin a kammala ta.
Ya bayyana cewa ɗaya daga cikin manyan nasarorin da gasar ta samar ita ce yadda ta fito da hazakar yarinya mai lalurar gani ga duniya, lamarin da ya ja hankalin jama'a da gwamnatin jihar.
Sakamakon haka, Gwamnan Jihar Yobe, Hon. Mai Mala Buni, ya bayar da umarnin a nemo wa yarinyar maganin idanunta a duk asibitin da ya dace domin a duba yiwuwar dawo mata da gani.
Abubakar K. Zaid ya ce idan har gasar ta zama silar da za ta taimaka wa rayuwar wannan yarinya da makomarta, to wannan kaɗai babbar nasara ce ga gasar da al'umma baki ɗaya.
Ya ƙara da cewa manufar Yobe Spelling Bee ba wai gano zakarun rubutun kalmomi kawai ba ce, har ila yau tana gano hazaka, ƙarfafa ilimi, da buɗe ƙofofin dama ga matasa domin su cimma burinsu.
Hakika, wasu lokuta amfanin gasa ba kofi ko lambar yabo kaɗai ba ne, illa canza rayuwar mutum baki ɗaya. ❤️📖✨🏆
Comments
Post a Comment