Tambayar da ake yawan yi a kwanakin nan ita ce — Shin Najeriya tana da tsarin kariya daga hare-haren sama (Air Defense System)?
Potiskum Media News ta yi bincike domin fayyace gaskiya ga jama’a.
A zahiri, Najeriya tana da wasu na’urorin tsaron sama, amma ba cikakkun Integrated Air Defense Systems (IADS) kamar irin na ƙasashen da suka ci gaba kamar Amurka, Rasha, ko China ba.
Tsarin kariyar saman Najeriya yana karkashin Nigerian Air Force (NAF), wacce ke da sassan da ke lura da tsaron sararin samaniya da kare iyakokin ƙasa daga duk wani hari ta sama.
Ga jerin wasu muhimman kayan tsaro da Najeriya ke da su:
1. Radar Systems: Najeriya na da Primary da Secondary Radar Stations a wasu yankuna domin gano jiragen da ke shiga sararin ƙasarta.
2. Surface-to-Air Missiles (SAMs): Rahotanni sun nuna NAF ta sayi wasu ƙananan SAM launchers daga China da Ukraine don kariya a manyan sansanonin soja.
3. Anti-Aircraft Guns: Rundunar soji tana da ZU-23 da Oerlikon GDF systems, waɗanda ake amfani da su wajen kare manyan wurare daga hare-haren sama masu nisa.
4. Jet Fighters: Sojojin saman Najeriya suna amfani da jirage irin su JF-17 Thunder daga Pakistan da Alpha Jets, waɗanda ke da ƙaramin ƙarfin tsaro ta sama.
Sai dai masana sun bayyana cewa tsarin kariyar saman Najeriya bai haɗu gaba ɗaya a matsayin “Air Defense Network” ba, ma’ana, ba dukkan na’urori suke haɗe cikin tsarin kwamfuta guda da ke lura da dukkan sararin ƙasa ba.
Wani tsohon hafsan sojin sama, Air Commodore Ibrahim Adamu (rtd), ya bayyana cewa:
> “Muna da kayan kariya daga hare-haren sama, amma ba cikakken tsarin haɗin kai ba. Abin da ake buƙata shi ne a haɓaka tsarin gano hari da kai farmaki kafin a shigo da jirgin abokan gaba.”
Najeriya tana da na’urorin tsaron sama, amma ba cikakken “Air Defense System” ba tukuna. Gwamnati tana ci gaba da haɓaka rundunar sojin sama da haɗa kai da ƙasashen waje domin inganta tsaro da kare sararin ƙasa daga duk wata barazana ta sama.
📸 Rahoton: Potiskum Media News
✍️ Edita: Sunusi Muhammad Musa
Comments
Post a Comment