Yadda Nuraddeen Ya zubda hawaye Lokacin Da Aka Hana Shi Aure, Yanzu Ya Zama Attajiri Bayan An Saki Budurwar.
Labarin wani matashi mai suna Nuraddeen ya zama abin koyi na tabbatar da ƙaddara da kuma ikon Allah na canza rayuwa. Labarin yana nuna yadda son zuciya da son duniya a cikin neman aure ke haifar da da na kuɗaɗɗa.
Nuraddeen, wanda a wancan lokacin ya kasance yana ƙoƙarin neman aure da farawa, ya fuskanci babban mataki a lokacin da ya tafi gidan masoyiyarsa da nufin tsayar da magana. A maimakon farin ciki, abin da ya samu shine magana mai zafi da takaici, wanda ya fito daga bakin budurwar tasa.
A cikin wata tattaunawa ta musamman da Potiskum Media News, Nuraddeen ya bayyana wannan lokacin mai raɗaɗi:
"Iyayen yarinyar sun ce ta kyale ni saboda bana da kuɗi, kuma suka tambaye ta 'Me zata ci a jikina?' Ita ce take faɗa min haka. Wallahi sai da na zub da hawaye. Na ce mata Allah ne Mai bayarwa da hanawa, sai kawai ta ce in yi haƙuri sannan ta shiga gida."
Nuraddeen ya daɗe a bakin ƙofar gidan a tsaye, jikinsa ya kasa motsawa saboda tsananin baƙin ciki da wulakanci.
Bayan kwana biyu da faruwar lamarin, Nuraddeen ya ba wa mahaifiyarsa labarin abin da ya faru. Mahaifiyar, a maimakon ta nuna fushi, ta rungume shi, ita ma ta zubar da hawaye, sannan ta yi masa nasiha mai ƙarfi:
"Ta ce, 'Ka yi haƙuri, wata rana za ka zama abin kwatance Insha Allah, ko bayan bana da rai.' Haka ta mun addu'a."
Da wannan addu'a da kuma watsi da soyayyar, Nuraddeen ya tattara hankalinsa wajen neman abin dogaro da kai. A hankali, ya manta da masoyiyar tasa.
Bayan shekaru da yawa, Allah ya buɗe wa Nuraddeen, kuma ya samu "rufin asiri fiye da yadda ban taɓa zato ba." A daidai wannan lokaci, matar da ta yi watsi da shi saboda talauci ta fuskanci nata gwajin rayuwa: Mijinta mai kuɗi, wanda ta aura, ya sake ta.
Makon da ya gabata ne, labari ya canza gaba ɗaya.
Nuraddeen ya ce: "Yanzu tazo shagona inda nake kasuwanci. Mungaisa lafiya. Tace mun, 'Ka yi aure kuwa?' Na ce, 'A'a.' Sai tace mun samun number ka. Nasa mata. Tayo mun text na ban haƙuri kan abin da ya faru a baya."
Labarin Nuraddeen ya zama muhimmin darasi ga matasa maza da mata a faɗin ƙasar nan. Ya nuna cewa neman aure da kuɗi kawai, ba tare da la’akari da ɗabi’a, juriya, da kuma ikon Allah ba, na iya zama babban kuskure.
Potiskum Media News na kira ga iyaye da matasa da su sani cewa arziki ba hannun mutum yake ba. Haƙuri da kuma addu’ar uwa sune mabuɗan nasarar rayuwa, fiye da abin duniya. Yanzu dai an bar Nuraddeen da zaɓi: ya yarda da uzurin budurwar tasa, ko ya ci gaba da rayuwarsa.
Muna kira ga masu karatu: Shin da kuna matsayin Nuraddeen, za ku yafe mata ku aureta, ko za ku ci gaba da rayuwarku? Ku rubuta ra'ayoyinku a shafinmu na sada zumunta!

Thank you Phataskum Media News for watching my story
ReplyDelete