Bankin Duniya (World Bank) ya fitar da sabon rahoto mai cewa yawan jama’ar Najeriya zai ƙaru zuwa miliyan 350 nan da shekarar 2050, abin da ke nuni da ƙaruwa sosai daga miliyan 220 da ake da su a halin yanzu.
A cewar Shugaban Bankin Duniya, Ajay Banga, wannan ƙaruwa tana nuna cewa Najeriya — wacce ke da yawan matasa — na da damar da za ta iya amfani da ita wajen gina tattalin arzikinta, muddin an tsara dabarun ci gaba da horar da matasa yadda ya kamata.
> “Najeriya tana da babbar damar da za ta iya amfani da ita domin ci gaban ƙasa, amma hakan zai tabbata ne idan gwamnati ta samar da yanayi da matasa za su iya yin aiki da basirarsu,” in ji Banga.
Sai dai masana sun yi gargadin cewa idan ba a kula ba, irin wannan ƙaruwa na iya haifar da matsaloli a fannin aikin yi, ilimi, kiwon lafiya, da ababen more rayuwa.
Bankin Duniya ya bayyana cewa ƙasashe da dama a nahiyar Afrika, musamman Najeriya, suna bukatar ƙara zuba jari wajen inganta rayuwar jama’a da samar da ƙarin dama ga matasa domin kauce wa koma baya.
Rahoton ya nuna cewa karuwar jama’a a Najeriya na iya zama albarka idan aka yi amfani da damar matasa wajen gina ƙasa da haɓaka tattalin arziki.
Rahoto daga: Potiskum Media News

Comments
Post a Comment