Skip to main content

Miye Makomar Faruk Umar da Hukumar Tace Finafinai ta Kama?

A ranar 18 ga Oktoba, 2025, Hukumar Tace Finafinai da Ɗab’i ta Jihar Kano ta kama Faruk Abubakar bisa zargin wallafa hotuna da rubuce-rubucen batsa a shafinsa na sada zumunta. Rahotanni sun tabbatar da cewa an kama shi ne a ofishin 'yan sanda na Bompai, Kano, bisa umarnin hukumar karkashin jagorancin Abba Mustapha Inuwa.

Bashir Musa Jammaje, wani abokin Faruk, ya tabbatar da sahihancin labarin bayan ya tuntubi Faruk da kansa, sannan daga bisani ya kira shugaban hukumar, Abba Mustapha, wanda ya tabbatar masa da cewa lamarin gaskiya ne. Ya kuma bayyana cewa hukumar ta jima tana kiran Faruk saboda irin wallafe-wallafen batsa da yake yi a shafukansa na sada zumunta, amma ya kasa amsa kiran da suke yi masa. Saboda haka, hukumar ta ɗauki matakin haɗa hannu da jami’an tsaro don kamo shi domin ya amsa tambayoyi.

Bashir ya roƙi hukumar da ta yi sassauci a kan Faruk, yana mai tabbatar da cewa za a duba lamarin cikin adalci. Ya kuma yi kira ga masu amfani da kafafen sada zumunta, musamman a Kano, da su guji wallafa abubuwan da suka sabawa tarbiyya da dokokin jihar, tare da mutunta hukumomin gwamnati.

Comments

Popular posts from this blog

Hon Ibrahim Mohammed Ibbiyo yayi tsokaci kan sakataren Gwamnati Baba Malam Wali inda yayi zargin cewa bai cika wasu muhimman sharuɗɗa na jagoranci ba...

  Cikakken Rahoto Wani jigo a jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a Yobe State, Ibrahim Mohammed Ibbiyo, ya yi zargin cewa ana ƙoƙarin ɗora magajin Gwamna Mai Mala Buni gabanin zaɓen 2027, yana mai gargadin cewa duk wani yunƙuri na kauce wa dokokin jam’iyya da tsarin zaɓe zai fuskanci ƙalubale a kotu. A cikin wata sanarwa mai taken “Yobe 2027 and the Search for a Credible Successor”, Ibbiyo ya soki wani rahoto da aka wallafa a Daily Trust, yana mai cewa rahoton na da nasaba da tallata wasu ‘yan takara da ake ganin gwamnati na marawa baya. Ya bayyana cewa al’ummar jihar na buƙatar shugaba mai ƙwarewa, gaskiya da hangen nesa, ba wanda aka fifita ta hanyar “godfatherism” ko don kare wasu muradun ƙalilan ba. Ibbiyo ya lissafa wasu daga cikin ‘yan takarar da yake ganin sun fi cancanta, ciki har da Ibrahim Mohammed Bomai, Ahmad Ibrahim Lawan da kuma Kashim Musa Tumsah, yana mai cewa suna da gogewa da kwarewar jagoranci. Ya kuma yi tsokaci kan Sakataren Gwamnatin Jihar, Baba Malam W...

Meyasa Zohran Mamdani yake goyon bayan Auren Jinsi?

‎Zaɓen Zohran Mamdani a matsayin Magajin Garin New York a shekarar 2025 ya haifar da muhawara mai zafi, musamman game da yadda ra'ayoyinsa na siyasa, masu ra'ayin ci gaba, suka haɗu da addininsa na Musulunci. ‎Duk da cewa Mamdani Musulmi ne da aka zaɓa a babban muƙamin siyasa a Amurka, ya bayyana sarai kuma a fili goyon bayansa ga haƙƙoƙin al'ummar LGBTQ+, ciki har da auren jinsi ɗaya (same-sex marriage). ‎Goyon bayan Mamdani ga ƙungiyar LGBTQ+ ya samo asali ne daga akidarsa ta Democratic Socialism, wadda ke mai da hankali kan daidaito, adalci na zamantakewa, da kuma karewa ga duk al'ummomin da ake warewa. ‎A matakin siyasa a Amurka, wannan ra'ayi na goyon bayan auren jinsi ɗaya ya zama daidaitacce ga 'yan siyasa masu ra'ayin ci gaba, kuma Mamdani ya ɗauki wannan matsayi a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarinsa na samar da New York wacce ta ke da adalci ga kowa: ‎Matakin da Ya Ɗauka: A cikin shirin yakin neman zaɓensa da kuma matsayinsa a Majalisar Dokokin Jihar...

Yadda Nuraddeen Ya zubda hawaye Lokacin Da Aka Hana Shi Aure, Yanzu Ya Zama Attajiri Bayan An Saki Budurwar.

 Labarin wani matashi mai suna Nuraddeen ya zama abin koyi na tabbatar da ƙaddara da kuma ikon Allah na canza rayuwa. Labarin yana nuna yadda son zuciya da son duniya a cikin neman aure ke haifar da da na kuɗaɗɗa. ‎Nuraddeen, wanda a wancan lokacin ya kasance yana ƙoƙarin neman aure da farawa, ya fuskanci babban mataki a lokacin da ya tafi gidan masoyiyarsa da nufin tsayar da magana. A maimakon farin ciki, abin da ya samu shine magana mai zafi da takaici, wanda ya fito daga bakin budurwar tasa. ‎A cikin wata tattaunawa ta musamman da Potiskum Media News, Nuraddeen ya bayyana wannan lokacin mai raɗaɗi:  ‎"Iyayen yarinyar sun ce ta kyale ni saboda bana da kuɗi, kuma suka tambaye ta 'Me zata ci a jikina?' Ita ce take faɗa min haka. Wallahi sai da na zub da hawaye. Na ce mata Allah ne Mai bayarwa da hanawa, sai kawai ta ce in yi haƙuri sannan ta shiga gida." ‎Nuraddeen ya daɗe a bakin ƙofar gidan a tsaye, jikinsa ya kasa motsawa saboda tsananin baƙin ciki da wulakanci. ‎B...