Hukumar Tace Finafinai ta Kano ta kama Faruk Abubakar bisa zargin wallafa hotuna da rubuce-rubucen batsa
RAHOTO: Hukumar Tace Finafinai ta Kano ta kama Faruk Abubakar bisa zargin wallafa hotuna da rubuce-rubucen batsa
Rahotanni daga Kano sun tabbatar da cewa Faruk Abubakar ya shiga hannun jami’an tsaro tun daren jiya, inda ake tsare da shi a ofishin ‘yan sanda na Bompai, bisa umarnin Hukumar Tace Finafinai da Ɗab’i ta Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Abba Mustapha Inuwa.
Wani abokin Faruk, Bashir Musa jammaje, ya bayyana cewa ya tabbatar da sahihancin labarin bayan ya tuntubi Faruk da kansa, sannan daga bisani ya kira shugaban hukumar, Abba Mustapha, wanda ya tabbatar masa da cewa lamarin gaskiya ne.
A cewar Bashir Jammaje, hukumar ta jima tana kiran Faruk saboda irin wallafe-wallafen batsa da yake yi a shafukansa na sada zumunta, amma ya kasa amsa kiran da suke yi masa. Saboda haka, hukumar ta ɗauki matakin haɗa hannu da jami’an tsaro don kamo shi domin ya amsa tambayoyi.
Jammaje ya ƙara da cewa bisa ƙa’ida, hukumar na fara gayyatar wanda ya saɓa dokarta domin a yi masa gargaɗi, amma idan ya ƙi zuwa, sai su haɗa shi da ‘yan sanda, kuma idan lamarin ya wuce wannan mataki, dole sai kotu ta shiga tsakani.
Sai dai duk da wannan, Bashir ya roƙi hukumar da ta yi sassauci a kan Faruk, yana mai tabbatar da cewa za a duba lamarin cikin adalci.
Ya kuma yi kira ga masu amfani da kafafen sada zumunta, musamman a Kano, da su guji wallafa abubuwan da suka sabawa tarbiyya da dokokin jihar, tare da mutunta hukumomin gwamnati.
“Kano fa ba Lagos ko Kaduna bace,” in ji Bashir Jammaje. “Dole ne mu mutunta doka da oda.”
Allah ya kyauta gaba, amin.
Rahoto daga Potiskum Media News

Comments
Post a Comment